27 Afirilu 2021 - 12:38
Zarif, Ya Yaba Da Kyakyawar Alakar Dake Tsakanin Iran Da Irak

Ministan harkokin wajen Iran, Muhammad Jawwad Zarif, wanda ke ziyara a Iraki, ya yaba da kyakyawar alakar dake tsakanin mahukuntan Bagadaza da kuma na Tehran.

ABNA24 : Mista Zarif, ya yi fatan alakar dake tsakanin kasashen biyu zata ci gaba ta kuma taimaka wajen samar da zaman lafiya da tsaro a yankin.

Ya kuma isar da ta’aziya da jaje ga kasar Iraki, game da mummunar gobarar data yi ajalin mutane da dama a wani asibitin Bagadaza.

Yayin ziyarar tasa Zarif, ya gana da shugaban kasar Irakin Berham Salih, ya kuma gana da takwaransa Fuad Hussein.

342/